Turkiyya za ta yi sulhi da Rasha

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Turkiyya ta harbo jirgin Rasha ne bayan ya keta sararin samaniyarta.

Firai Ministan Turkiyya Ahmet Davutoglu ya ce kasarsa za ta hada gwiwa da Rasha da sauran abokanta domin yayyafa ruwa kan wutar rikicin da ke tsakaninsu bayan ta harbo jirgin yakin Rasha a Syria.

Mista Davutoglu, wanda ya bayyana haka a wata makala da ya wallafa a jaridar Times ta Biritaniya, ya ce babban abin da ya kamata su sanya a gaba shi ne yaki da 'yan kungiyar IS.

Sai dai ya ce dole ne Turkiyya ta kare iyakokinta.

Rasha dai ta ce jirgin Turkiyya samfurin F-16 ya harbo jirgin samanta samfurin SU-24 a kan iyakar Syria da gangan, ko da ya ke Turkiyya ta ce ta yi hakan ne bayan da ta gargadi matuka jirgin cewa suna keta sararin samaniyarta.

Wasu 'yan bindiga a Syira sun kashe daya daga cikin matuka jirgin Rashan, wanda ya fice daga jirgin a lokacin da aka harbo shi.