Kamaru:Harin bakin wake ya kashe mutane biyar

Hakkin mallakar hoto .

Wasu 'yan mata 'yan kunar baki wake sun ta da ban a Dabang da ke arewacin Kamaru.

Rahotanni na cewa 'yan matan biyu dauke da bama-bamai sun kai harin ne a kan wani shago da kuma wani gida a garin Dabang da ke arewacin kasar a inda suka hallaka mutane 5 suka kuma jikkata wasu 12

Wani jam'in sojin kasar kanar Jacob Kodji ne tabbatar da labarin sannan ya kara da cewa 'yan kunar bakin waken 'yan Najeriya wadanda su ka shigo kamaru a matsayin 'yan gudun hijira.

A kwankin baya Kamaru ta kori dubban 'yan gudun hijira daga Najeriya.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakkin kai harin sai dai salon hari yayi kama da na 'yan kungiyar Boko Haram wacce ke hare-hare a Najeriya da kamaru da Niger da kuma Chad.