An yi jana'izar Dan Wanzam

Image caption Ranar Asabar aka yi jana'izar Muhammadu Danmalam, wato Dan Wanzam

An yi jana'izar wani dadadden dan wasan kwaikwayon barkwanci a Najeriya, wanda aka fi sani da Dan Wanzam; ya rasu ne ranar Jumu'a da dare.

Alhaji Muhammadu Danmalam ya rasu ne yana da shekaru 104 a gidansa da ke birnin Sakkwato a arewa maso yammacin kasar.

"Ya rasu ne bayan ya kwashe kusan shekara daya da rabi yana jinya a asibitoci daban-daban", inji dansa, Abubakar Danmalam, a wata hira da BBC Hausa.

Marigayi Dan Wanzam ya yi fice ne a wasan kwaikwayon Idon Matambayi wanda gidan talabijin na kasa, NTA, ya rika nunawa a shekarun1980 zuwa 1990.

Wasan kwaikwayon, wanda aka yi a harshen Hausa, ya kunshi barkwanci da fadakarwa.

Karin bayani