An kashe 'yan sanda hudu a Masar

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Hari a Masar

Wasu 'yan bindiga da suka rufe fuskokinsu wadanda su ka je a kan babur sun harbe wasu 'yan sanda hudu a kudancin Alkahira.

'yan sanda na tsaye ne a wajen binciken ababan hawa da ke kusa da dalar da masu yawon bude idanu ke zuwa a Giza.

Tuni masu bincike su ka ziyarci wurin da abin ya faru.

Wasu rahotanni sun ce maharan sun sace makaman 'yan sandan.

Masu tsatstsauran ra'ayin addinin islama a Masar sun kashe 'yan sanda da sojoji da dama kana sun kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati tun bayan da sojoji suka karbi mulkin kasar a hannun shugaba Mohammed Morsi a shekarar 2013.