Ni zan sake lashe sabon zabe— David Mark

Sanata David Mark Hakkin mallakar hoto senate website
Image caption Sanata David Mark

Tsohon shugaban majalisar dattijai a Najeriya, David Mark ya bukaci jama'ar mazabarsa da kada su tayar da fitina sakamakon soke zabensa da wata kotu ta yi.

A cikin wata sanarwa, Sanata Mark ya bukaci jama'ar mazabar sa da kada su karaya, a maimakon haka, su kara shiri na tunkarar zaben da za a sake gudanarwa.

Ya ce yana da yakinin zai sake lashe zaben idan aka sake gudanar da shi.

Wata kotun daukaka kara ce da ke zama a Makurdi babban birnin jihar Benue ta soke zaben da aka yiwa Sanata David Mark.

Kotun ta ce akwai kuskure a matsayin da hukumar zabe ta kasar INEC ta dauka na baiyana David Mark, dan takarar Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben yan majalisar dattijai a shiyyar kudancin Benue wanda aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris

Dan takarar sanata a karkashin jam'iyyar APC shiyyar kudancin Benue Donald Onjeh shi ne ya shigar da karar.

Kotun ta bayar da umarnin a sake zaben kujerar majalisar dattijan cikin kwanaki casa'in.