Ban mutu ba — Ali Nuhu

Image caption Ali Nuhu fitaccen jarumin shirin fina-finan Hausa ya nuna takaicinsa dangane da karyar mutuwa da aka yi masa.

Fittaccen dan wasan fina-finan Hausa Ali Nuhu ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa wasu 'yan fashi sun shiga gidansa da ke Kano, suka hallaka shi.

Jarumin ya nuna takaicinsa da wadannan rahotanni tare da bakin cikin yadda wadanda suka kitsa labarin suka sa 'yan uwa da abokan arziki da kuma masoyansa a cikin damuwa.

Alu Nuhu ya kara da cewa lafiyarsa kalau, kuma a halin yanzu yana Jos a jihar Plateau, inda yake aikin daukar wani fim.

A ranar Alhamis ne aka soma yada jita-jitar mutuwar jarumin a shafukan sada zumunta na intanet.