Kenya:An kama wasu masu shirin kai hari

Yan sandan Kenya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yan sandan Kenya

Yan sanda a Nairobi babban birnin kasar Kenya sun kama mutane biyu wadanda suka ce gungun yan leken asiri na kasar Iran sun dauke su aiki da nufin kai hari a cikin birnin.

Shugaban rundunar yan sandan na Kenya Joseph Boinett yace mutanen sun ziyarci Iran sau da dama kuma an basu kudi da jadawalin wuraren da za su kai hari.

Yace an kuma bukaci su dauki sabbin mutane ciki har da yara yan makaranta.

Mr Boinett yace wadanda ake zargin sun bai wa yan sanda muhimman bayanai game da shirin da suka tsara.