An kai hari sansanin sojin MDD a Mali

Sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali

Wasu yan bindiga da ake kayutata zaton masu da'awar jihadi ne sun kashe mutane uku ciki har da sojoji biyu yan kasar Guinea da ke aikin wanzar da zaman lafiya karkashin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali.

Wasu mutane goma sha hudu kuma sun sami raunuka.

Yan bindigar sun kai hari ne wani sansani na sojin Majalisar Dinkin Duniyar a arewacin Mali.

Wani mai magana da yawun rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Dunia a Mali yace rokoki hudu zuwa biyar ne suka fada cikin sansanin da ke Kidal.

Sojojin Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya suna kokarin tabbatar da zaman lafiya a Mali wadda Faransa ta yiwa mulkin mallaka wadda kuma kungiyoyin masu ikrarin jihadi suka kutsa cikinta.

Kwanaki takwas da suka wuce wasu yan bindiga suka kai hari wani otel a Bamako babban birnin kasar Malin inda suka kashe mutane goma sha tara.