Yan bindiga sun sako mahaifiyar Siasia

Samson Siasia
Image caption Samson Siasia

An sako mahaifiyar mai horar da yan wasan Najeriya yan kasa da shekaru 23 Samson Siasia bayan da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da ita kwanaki 12 da suka wuce.Wasu yan bindiga su uku suka sace Ogere Siasia daga gidan iyalanta dake jihar Bayelsa mai arzikin mai a yankin Niger Delta inda garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ke cigaba da yawaita.

Siasia wanda ke kasar Senegal tare da yan wasa domin gasar kwallon kafa ta cin kofin Afirka yan kasa da shekaru 23 ya shaidawa BBC cewa ya yi farin ciki da aka sako mahaifiyarsa lafiya.

A ranar Asabar din nan da safe yan bindigar suka sako Madam Ogere.

Tun da farko yan bindigar sun bukaci a biya su Naira miliyan 150 daga baya suka rage zuwa Naira miliyan 50 sannan zuwa Naira miliyan 35

Babu tabbas ko an biya kudin fansa kafin a sako dattijuwar mai shekaru 72 a duniya.

Yan sanda a Bayelsa sun ce har yanzu suna ci gaba da farautar wadanda suka yi garkuwa da ita.