Erdogan ya yi nadamar harbo jirgin Rasha

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan yace ya yi nadama da harbo jirgin yakin Rasha da Turkiyar ta yi a kusa da iyaka da Syria, sai dai kuma bai nemi afuwa ba.

Ya shaidawa wani taro a Balikesir cewa yayi fatan a ce lamarin na ranar Talata bai faru ba yana mai cewa hakan ba zai sake faruwa ba.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ki yarda ya tattauna batun da Mr Erdogan har sai ya nemi afuwa.

Moscow na shirin kakabwa Turkiya jerin takunkumin karya tattalin arziki, ta kuma takaita zirga zirgar yan yawon bude ido.

A waje guda kuma Turkiya ta gargadi yan kasarta su guji dukkan wata tafiyar da ba ta zama dole ba zuwa Rasha.