An yi wa kamfanin Vtech kutse

Image caption Kayan da kamfanin Vtech ke kerawa

An yi wa kamfanin Vtech wanda ke kera kayan latironik na wasa da karatu na yara kutse a manhajar runbun adana bayanansa ta Learning Lodge.

Kamfanin ya ce wasu sun shiga cikin rumbum bayansa batare da izini ba a ranar 14 ga watan Nuwamba.

Manhajar ta Learning Lodge wata hanya ce da masu mu'amala da kamfanin ke sauke wasannin kwamfuta a wayoyin su, da kuma litattafai da sauran abubuwa.

Babu masaniya ko mutane nawa kutsen ya shafa, amma wasu sun shaida wa BBC sun samu sakonnin email akan cewa an abin ya shafe su.

An ga wasu bayanai masu yawa a shafin intanet da ake gani wadanda suka yi kutsen ne suka sanya su, kuma daga baya aka boye su.

Wasu kwararru sun ce daga cikin bayan da aka sata, sun hada da sunayen yara, da kwanakin wata da kuna ranakun haihuwan masu mu'amala da kanfanin, da jinsinsu.

Jami'an kanfanin sun ce yana da kyau a fahimci cewa babu bayan katin biyan kudi na mutane a cikin rumbun da aka yi wa kutse.