EU ta nemi taimakon Turkiya kan yan cirani

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugabannin tarrayar turai za su gana da Firaministan Turkiya a Brussels nan gaba a yau inda suke fatan sanya hannu akan wata yarjejeniya da nufin dakile kwararowar yan cirani zuwa kasashen turai.

An fahimci kungiyar tarayyar turan za ta baiwa Turkiya Euro Biliyan ukudomin taimaka mata daukar dawainiyar dumbin gudun hijirar Syria a kan iyakokinta.

Domin saka wa wannan farar aniya da kuma sauran damammaki za a bukaci a na ta bangaren Turkiya ta kara himma wajen hana yan cirani kaiwa tsibiran Girka.

Sai masu aiko da rahotanni sun ce har yanzu ba a cimma matsaya a kan cikakken jadawalin yarjejejeniyar ba kuma lamuran sun kara rincabewa sakamakontsamin dangantaka tsakanin Turkiya da Rasha game da batun Syria.