Paparoma Francis ya yi kiran a samu hadin kai a CAR

Image caption Paparoma Francis

Fafaroma Francis ya yi a samu hadin kai da fahimtar juna a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Kasar dai ta sha fama da rikice-rikice a tsakanin musulmai da Kiristoci.

Daruruwan mutane suka yi jerin gwano a kan hanyar zuwa filin jiragen saman kasar domin tarbar Paparoman.

Kana wasu mutane sun rera waka a loakcin da ya isa sansanin 'yan gudun hijra.

Ana kyautata tsammanin Paparoman zai gana da shugabannin al'ummar musulmai da ke kasar, sannan zai kai ziyara wani Masallaci.

Shugabannin Musulmai da Kiristoci a jamhuriyar tsakiyar Afrika sun ce kasancewar Paparoman a kasar, zai iya taimakawa wajen bada damar tattaunawa da kuma rage tashe-tashen hankula a yayin da zaben kasar ke karatowa.