Paparoma Francis ya isa Congo

Paparoma Francis
Image caption Paparoma ya fara ziyarar wasu daga cikin kasashen Afurka .

A jawabin da ya yi a sansanin 'yan gudun hijira a Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo, Paparoma Francis ya ce fatan sa shi ne a samu zaman lafiya. Daga nan kuma sai ya jagoranci rera wata waka mai taken ''Mu 'yan uwa ne''.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da Paparoman ke kai wa daya daga cikin kassahen Afurka da ke fuskantar rikice-rikice masu nasaba da addini da kabilanci.

Dubban mutane ne su kai dandazo tare da jerin gwano tun daga filin jirgin saman kasar, zuwa manyan tituna a lokacin da Paparoma Francis ya isa.

Haka ma titunan babban birnin kasar Bangui ya cika makil da mutane ana ta shagulgulan wanna ziyara.

Ana sa ran Paparoman zai gana da shugabannin addinin Musulunci a kasar da ziyartar wani masallac a gobe Litinin.

A bangare guda kuma shugabannin addinan biyu, su na fatan wanann ziyara ta wanzar da zaman lafiya tsakaninsu tare da kawo karshen rikicin da ake yi gabannin babban Zaben da za a yi a Congon a watan gobe.