Mata za su fara tsayawa takara a Saudia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matan Saudia

A karon farko mata a kasar Saudi Arabia sun fara wani gangami domin neman gurbi a ofisoshin gwamnati.

Kimanin mata dari tara ne su ka tsaya takarar shugabancin kananan hukumomi a zaben da za ayi a kasar a cikin watan gobe.

Kuma wannan shi ne karo na farko da mata za su zabi jami'an gwamnati a kasar.

Domin kiyaye dokokin da kasar ta tanadar, ba za a kyale maza da mata su kada kuri'a a wuri guda ba.

Kuma saboda mata ba za su bude fuskokinsu a bayyanar jama'a ba, an hana maza ma lika hotunan su a ko ina domin yakin neman zabe.