Turkiya za ta mika gawar matukin Rasha

Matukin jirgin Rasha da Turkiya ta harbo Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Matukin jirgin Rasha da Turkiya ta harbo

Turkiya ta ce ta dauko gawar matukin jirgin Rasha bayan da aka harbo jirgin a kan iyakar Syria kuma ta na shirin mayar da gawar zuwa Rasha.

Yan tawayen Syria ne suka harbi matukin yayinda ya yi kokarin kubuta da rigar lema bayan da Turkiya ta harbo jirginsa da makami mai linzami.

An sami ceto matuki na biyu.

Lamarin ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Turkiya.

A ranar Juma'a Moscow ta baiyana kakabawa Turkiya jerin takunkumi a matsayin ramuwar gayya.