Nigeria: EFCC ta kama Bashir Yuguda

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption EFCC ta kama Bashir Yuguda ne game da wani kudi daga ofishin Sambo Dasuki

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC, ta kama tsohon minista a ma'aikatar kudi ta kasar, Bashir Yuguda.

Wata majiya a hukumar ta EFCC ta tabbatar wa BBC cewa tsohon ministan na hannu tun da rana, kuma har yanzu yana ofishinta yana amsa tambayoyi.

Tare da Bashir Yugudan, hukumar ta EFCC ta kuma kama wadansu manyan jami'ai na Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara a kan Sha'anin Tsaro, NSA.

Ana yi wa jami'an tambayoyi ne game da badakalar yin sama-da-fadi da wadansu kudaden sayen makamai da ake zargin tsohon Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Sambo Dasuki da aikatawa, zargin da ya musanta.

Wadansu kafofin yada labarai na Najeriya sun ambato wata majiya tana cewa an tura wa Bashir Yuguda wadansu makudan kudade da suka kai biliyoyin naira daga ofishin na NSA, kuma tsohon ministan ya kasa yin gamsasshen bayani a kan dalilan tura kudin asusunsa na banki.

Majiyar ta kara da cewa an tura kudin ne a tsakanin watan Disamban 2014 da watan Mayun 2015.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani a hukumance daga hukumar ta EFCC dangane da kame tsohon ministan kudin.

Karin bayani