Mutane 6 sun mutu a rikicin kurkuku a Guatemala

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gungun bata gari a Guatemala

Jami'ai a Guatemala sun ce an kashe akalla mutane 6 a lokacin da rikici ya barke a wani gidan kurkuku a kasar.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin firsinonin dake gidan yarin da fadan ya kaure, suna dauke da bindigogin AK 47.

An tura jami'an 'yan sanda da sojoji na musanman domin kwantar da tarzomar a gidan yarin wanda yake nisan kilometa 65 a kudu da babban birnin kasar.

Fiye da firsinoni dubu 3 ne ake tsare da su a gidan yarin, wanda ke da wuraren tsare mutane 600 kadai.