Paparoma ya ziyarci masallaci a Bangui

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paparoma Francis ya yi kira ga Musulmai da Kiristoci da su dinga kaunar juna.

Paparoma Francis ya kai ziyara wani masallaci a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, a bangare mafi wuya a ziyarar da yake yi a Afirka.

Paparoma ya gana da Musulman da suka samu mafaka a Bangui, bayan an kwashe kusan shekaru uku ana yaki tsakanin Musulmai da Kiristoci a kasar.

Da yake jawabi a masallacin na Koudoukou, Paparoma ya shaida wa Musulman cewa, "dole ne mu hada gwiwa domin kyamar masu nuna mana kiyayya, mu daina rikici da daukar fansa, musamman rikicin da wasu ke yi da sunan Allah".

Paparoma Francis ya bayyana Musulmai da Kiristoci a matsayin 'yan uwa, yana mai yin kira a gare su da su guji kyamar juna.

Akasarin Musulmai sun gudu daga Bangui, sai dai har yanzu akwai wasu 15,000 da ke ci gaba da zama a wani yanki mai suna PK5, inda Kiristoci 'yan bindiga suka yi musu kawanya.

Paparoma Francis zai kammala ziyararsa ne a birnin na Bangui, inda zai yi wani taron addu'oi.