An gano abin da ya sa jirgin AirAsia ya fadi

Image caption Bincike ya gano cewa matukan jirgin sun dagula al'amura a yunkurin da suka yi na hana shi faduwa.

Jami'ai a Indonesia sun ce wata na'ura da ta samu matsala ita ce babban dalilin da ya haddasa faduwar jirgin AirAsia a kogin Java, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji 162 a watan Disambar shekarar 2014.

Babban rahoton da aka fitar kan hatsarin jirgin ya gano cewa matakan da ma'aikatan jirgin suka dauka domin shawo kan lamarin sun kara ta'azzara lamarin ne kawai.

Jirgin, samfurin Airbus A320-200, ya tashi ne daga Surabaya zuwa Singapore, kuma ya bata minti 40 bayan ya tashi.

An fitar da rahoton ne bayan an kwashe kusan shekara guda ana yin bincike kan musabbabin hatsarin jirgin.