Kabore ya zama shugaban Burkina Faso

Tsohon firayiminstan Burkina Faso Mista Roch Christian Kabore ya lashe zaben shugaban kasar da babban rinjaye.

Mista Kabore ya lashe zaben ne da kashi 53.5 na yawan kuri'un da aka kada, abokin karawarsa Zephirin Dabre kuma a ya samu kashi 21 a cikin dari

Mr. Dabre ya aika sakon taya murna ga Mr. Kaboren tun kafin a sanar da sakamakon zaben a hukumance.

Zaben shi ne na farko tun lokacin da aka tuntsurar da Blaise Compaore wanda ya mulki kasar na tsawon shekara 27.

An dai shirya gudanar da zaben ne a wantan Satumba amma aka daga sakamakon juyin mulki da zaratan sojoji masu tsaron fadar shugaban kasar suka yi, wanda bai yi nasara ba.

Mista Kabore ya taba zama shugaban Jam'iyyar Congress for Democracy CDP kafin ya bar ta a shekarar 2014 bayan adawa da shirin tsawaita mulkin Blaise Compaore.

Zaben dai shi ya kawo karshen gwamnatin rikon kwaryada aka kafa bayan tumbuke Compaore.