An bukaci a kama George Bush

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Dick Cheney.

Kungiyar kare hakkokin bil-Adama ta Human Rights Watch ta ce a binciki tsohon shugaban Amurka George W. Bush da mataimakinsa Dick Cheney da wadansu manyan jami'an gwamnatinsa.

Human Rights Watch ta bukaci a tuhume su ne da hannu a laifin cin zarafin wadansu mutane da ake zargi da kitsa harin da aka kai Amurka ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001.

Kungiyar ta ce binciken da wani kwamiti na majalisar dattawa ya gudanar a bara ya nuna cewa Hukumar Leken Asiri ta CIA ta bayar da umurnin a azabtar da jama'a, lamarin da ya sa gwamnatin Obama ta kaddamar da bincike.

Hukumar leken asirin ta ce hanyoyin azabtarwar sun hada tsoma kan mutum a ruwa da hana su barci.