An yi musayar fursunoni a Syria

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan tawayen Nusra Front da ke kasar Syria.

'Yan tawayen Syria na Nusra Front, sun saki wasu sojojin Lebanon da suka kama a madadin wasu fursunoni da aka mika musu.

An kame sojojin na Lebanon su 16 ne fiye da shekara daya da ta gabata a garin Arsal da ke kan iyaka.

Lebanon ta musanya sojojin ne da wasu 'yan tawaye masu tsattsauran ra'ayin addini da suka kama su 13, cikin su har da tsohuwar mai dakin shugaban IS Abu Bakr al-Baghdadi mai suna Saja al-Duleimi.

Saja al-Duleimi ta ce sun jima da rabuwa da shugaban na IS, kuma ita yanzu za ta doshi kasar Turkiyya ne.