Amurka tana janye wa daga Mali

Hakkin mallakar hoto Radisson Blu Hotel
Image caption A watan jiya ne 'yan bindiga suka kai hari a Otal din Radisson.

Amurka tana ja da baya a alakar diplomasiyya da ke tsakaninta da Mali sakamakon matsalar tsaro da take ci gaba da ruruwa a kasar.

Yanzu haka Amurka za ta rinka gudanar da kwarya-kwaryar shirin diplomasiyya ne a tsakaninta Mali.

Hakan dai ya biyo bayan harin da kungiyar IS ta kai a Otal din da ke Bamako, babban birnin kasar ta Mali a watan jiya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20.

Wakiliyar BBC ta ce Ofishin harkokin cikin gidan Amurka ya ba da sanarwar cewa duk wani wanda ya san yana zaman jeka-na-yi-ka a ofishin huldar jakadancin Amurkar a Mali -- da ma sauran iyalai wadanda suke son komawa Amurka -- za su iya komawa gida.