'Yan sanda sun gargadi 'yan Biafra

Hakkin mallakar hoto Nnamdi Twitter
Image caption Nnamdi Kanu, daya daga cikin shugabannin masu fafutukar ganin an kafa jamhuriyar Biafra.

Babban sufeto janar na 'yan sanda Najeriya, Solomon Arase, ya gargadi kungiyoyin da ke neman kafa jamhuriyar Biafra MASSOB da IPOB, da su daina tayar da hankalin al'umma ko kuma su fuskanci fushin shari'a.

Wannan gargadi ya biyo bayan tashe-tashen hankula da kone-kone da 'yan sandan Najeriyar ta lura MASSOB din na yi.

Zanga-zangar da matasan suke gudanarwa na neman tarwatsa rayuwar al'umma, inda suka tsayar da kasuwanci da kawo tsaiko na abubuwan hawa.

Hukumomin sun jaddada cewa "Kwanciyar hankali da tsare rayuwar al'umma da kare muhalli su ne muhimman abubuwa da ke gaban hukumar 'yan sandan Najeriya"

Matasan dai sun yi kira da a saki daya daga cikin shugabannin su Nnamdi Kanu wanda kawo yanzu ya shafe watanni biyu a tsare kan laifin yi wa kasa zagon kasa.