Al'ummar Igbo a arewa ta soki Biafra

Hakkin mallakar hoto Nnamdi Twitter
Image caption Nnamdi Kanu mai fafutukar Biafra

A Najeriya, wasu 'yan kabilar Igbo da ke zaune a arewacin kasar sun bayyana rashin jin dadinsu dangane da ci gaba da zanga-zangar da masu neman kafa kasar Biafra ke yi.

Elder Steven Akoma, daya daga cikin shugabanin al'ummar Igbo mazauna jihar Sakkwato, ya shaida wa BBC cewa fafutukar da matasan suke yi ganganci ne, domin ba su san yadda aka kwashe ba lokacin da aka yi fafutikar kafa Biafra ta farko.

Ya ce ya kamata matasan da sauran masu goyon bayan kafa kasar Biafra su rungumi hanyoyin zaman lafiya da gwamnati domin cimma muradunsu.

Elder Akoma ya ce ba lallai ba ne a ce mutun zai ji dadi a kowacce gwamnati.

A 'yan makwannin nan dai, kungiyoyin da ke goyon bayan kafa Biafra sun yi ta gudanar da zanga-zanga, inda suka rufe wasu manyan hanyoyin yankin kudu maso gabashin kasar.

Tuni dai shugaban 'yan sanda a Najeriya ya bayar da umarnin tura karin 'yan sanda zuwa yankin na kudu maso gabas domin shawo kan masu zanga-zangar.