Ana bincike kan sace 'yan mata a Borno

A Najeriya, gwammnatin jihar Borno ta fara yin binciken kan rahotannin da ke cewa an sake sace wasu 'yan mata a garin Bamburatai da ke karamar hukumar Biu.

Mazauna garin dai sun shaida wa BBC a farkon wannan makon cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai musu harin, sannan suka yin awon-gaba da 'yan matan.

Kakakin gwamatin jihar Borno Isa Gusau ya shaida wa BBC cewa ko da ya ke ba su da cikakken bayani kan sace 'yan matan, amma sun nada kwamiti domin yin bincike kan lamarin.

Ya kara da cewa 'yan kwamitin -- wadanda suka hada da mutanen garin -- za su samu bayanai na hakika kan ko an sace matan, ko kuwa ba a sace su ba.

A cewarsa, sau da dama ana samun bayanan sace 'yan mata a jihar amma daga bisani za a gano ba haka ba ne.