Kotu ta umurci a gabatarwa jama'a da wasikun sirri na FBI

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata kotu ta yi karin haske a kan dubban wasiku da suka kunshi bayannan sirri kan tsaro da hukumar bincike ta FBI ta r aikewa kamfanonin internet a kowace shekera.

Takardun sun nuna yadda hukumar kan bukaci kamfanonin su samarta da adireshin e mail na mutane da ke gudanar da bincike akansu da kuma sauransu.

Sai dai hukumar ta FBI ba ta ce komai ba lokacinda BBC ta tuntubeta.

Alkalin wata kotu a birnin Newyork ya yanke hukunci a kan cewa a gabatarwa jama'a da wasikar da hukumar FBI ta rubuta a shekara ta 2004.

Mutumin da aka aikewa da wasikar, Nicholas Merril , wanda shi ne shugaban tsohon kamfanin shafin internet na Calyx shi ne ya shigar da kara inda ya ke tuhumar babban atoni janar da hukumar FBI da aikata ba dai dai ba.

Sai dai bayan shekaru goma sha daya da aka kwashe kotun na saurar karar ta yanke hukunci da ya nuna cewa hukumar FBI ta nemi a smar mata da bayannan da suka shafi cinikayya kan wasu kayayyaki da adireshin e mail na masu amfani da shafukan internet.