An kashe zakin da ya tsere a Jos

Hakkin mallakar hoto Mustapha
Image caption An kashe Zakin da ya tsere daga gidan namun daji na Jos.

'Yan sanda a Jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya sun bayyana cewar sun harbe wani gawurtaccen Zaki da ya gudu daga gidan ajiye namun daji da ke Jos babban birnin Jihar.

An kashe Zakin ne a zagayen wurin ajiyar dabbobin a Jos bayan da yunkurin kama shi ya ci tura.

'Yansanda sun ce an kashe Zakin ne don kar ya zamo hadari ga jama'a.

Wakilin BBC a yankin ya ce mutane da yawa sun yi tir da kashe Zakin, suna masu cewa kamata ya yi a yi amfani da allurar bacci a kama shi.

Zakin dai ya fice daga kejinsa ne a lokacin da ma'aikata suka bude kofarsa don ba shi abinci.