Zaki ya tsere daga gidan Zoo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zakin ya dade ajiye gidan ajiye namun daji da ake cewa 'Wild life park' da ke Jos, babban birnin jihar Filato.

Hukumomi a Jihar Filato dake arewa ta tsakiyar Najeriya sun bayyana cewa wani gawurtaccen zaki, ya kubuce daga gidan ajiye namun daji dake Jos, babban birnin Jihar.

Rahotanni dai na cewa zakin ya fice ne daga kejinsa da safiyar ranar Laraba, yayin da ake kokarin bashi abinci kamar yadda aka Saba.

Kakakin rundunar 'yan sanda a Jihar, DSP Abuh Emmanuel, ya shaida wa wakilin BBC cewa kawo yanzu ba a san inda zakin ya nufa ba, amma ya kara da cewa jami'an tsaro da ma'aikatan gidan ajiye dabbobin da sauran kwararru na ci gaba da kokarin gano inda dabbar take da kuma kamo ta.

Hukumomi a Jihar ta Filato dai sun ce ba a samu wani rahoto na cewa zakin ya yi ta'adi ba, amma sun yi kira ga jama'a a Jihar da su yi hattara.