Me ya sa Newscastle ke jan hankalin 'yan wasan Africa?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin wasan St James Park

A Newcastle wasan kwallon kafa shi ne kadai wasan da ake yi a garin.

Wasan kwallon kafa sarki ne a garin.

Ba kamar sauran biranen turawa ba kamar su Manchester da Birmingham da kuma Liverpool, Newscastle ta na da Kulob na 'yan wasanta, kuma a duk ranar da 'yan wasanta za su yi wasa komai tsayawa ya ke cak a garin.

Mutanen garin sun mayar da wasan kwallon kafa tamkar addini.

Kwallayen da Alan Shearer ya ci guda 206 a cikin shekaru 10 da ya yi yana buga wasa a filin wasa na St James Park, shi ya janyo wasan kwallon kafa ya kasance wasa daya tilo da ake yi a garin.

'Yan wasan Newcastle sun ja hankalin manyan 'yan wasan Afrika.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obafemi Martins ya bugawa Newcastle wasa

'Yan Kulob din na Newcastle sun ce ba za su taba mantawa da Habib Beye da Obafemi Martins ba.

Sannan dan wasa kamar Papiss Cisse wanda ke sa riga lamba 9 ya taka muhimmiyar rawa a Kulob din, ya kuma maye gurbin Alan Shearer ne.

A tsakanin shekarun 2001 zuwa 2002 akwai 'yan wasan Afrika a Kulob din Newcastle da suka hada da Shola Ameobi da kuma Lomana Lua Lua wanda ya fito daga jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

To ko me yasa Kulob din na Newscastle ke jan hankalin 'yan wasan Afrika?

Image caption Dusar kankara na zuba

Dalilin shi ne birnin Newcastle ya kasance wuri ne da ba bu hayaniya a ciki, sannan kuma yana da yanayi mai sanyi ta yadda za a iya yin gasar Primiya a ciki.

Mutane kamar Papiss Cisse na kaunar Newcastle, shima Cheick Tiote na kaunar Kulob din.

A baya 'yan wasa da dama na zuwa Newscastle kuma suna jin dadin zama a Kulon din.

To shin ko wanne dan wasan Afrika ne ya fi barin tarihi a Kulob din Newcastle?

Image caption Dan wasan Newcastle Papiss Cisse

Papiss Cisse shi ne, saboda akwai wani lokaci da akayi hira da shi ya ke cewa da a ce bai zama dan wasan kwallon kafa ba, da yanzu shi Masunci ne a Senegal.

Cheick Tiote kuwa na daga cikin 'yan wasan Afrika biyar da yanzu haka su ke tare da kulob din Newscastle.

Newcastle ta zamo kulob din da 'yan wasan Afrika ke rububin shiga tin daga shekarar 2000.