Matar Zuckerberg ta haihu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mark da matarsa, Pricillia da 'yarsu Max

Matar matashin nan da ya kirkiri shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg ta haihu.

Mark -- wanda ya sanar da hakan ta shafinsa na Facebook -- ya ce an haifa masa 'ya mace kuma ya rada mata suna Max.

Mista Zukerberg ya kara da cewa shi da matarsa Priscillia sun sha alwashin sadaukar da kashi 99 cikin dari na hannayen jarinsu a kamfanin wajen kyautata wa duniya domin 'yar tasa ta taso ba tare da ta fuskanci matsala.

Hakan yana nufin za su sadaukar da kudi kimanin dalar Amurka biliyan 45.

Ya ce kudaden za su tafi ne ta hanyar magance cututtuka da inganta harkar ilimi da yaki da gurbatar muhalli da kuma rage radadin talauci.