An kama jami'in Jami'ar China da cin hanci

Hakkin mallakar hoto Renmin University
Image caption An gurfanar da Jami'in Renmin University a gaban kuliya saboda karbar na Goro

Wani tsohon jami'i a bangaren daukar dalibai a babbar Jami'ar kasar China ya gurfana gaban kuliya sakamakon zarginsa da amsar cin hanci da ya kai fiye da dala miliyan uku da rabi.

An dai zargi Cai Rongsheng ne da karbar kudin domin ya bawa dalibai gurbin karatu a Jami'ar ta Renmin da ke Beijing.

Ya kuma bar wasu daliban su sauya kwasa-kwasan da suke yi .

Wannan badakala ta samun irin wannan matsala a Jami'oin China na daga cikin ta baya-bayan da ta faru.

Shugaban kasar ta China Xi Jinping ya yi alkawarin kawar da rashawa a tsakanin al'ummar kasar.