An bayar da belin Raymond Dokpesi

Hakkin mallakar hoto AIT
Image caption Shugaban gidan talabijan na AIT, Raymond Dokpesi.

Hukumar da ke hukunta masu yi wa arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC, ta bayar da belin shugaban gidan talabijan na AIT, Raymond Dokpesi.

EFCC ta tsare Dokpesin da tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa ne tun ranar Talata inda take tuhumar su game da batun binciken da take gudanarwa kan wasu kudade dala biliyan 2.1 da tsohon mai bai shugaban kasa shawarar kan harkokin tsaro ya yi amfani da su wajen sayan makamai lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Dokpesi dai ya samu belin bayan tambayoyi da akayi ta masa kan batun.

Ya ce "An bani belin ne jiya, kuma suka bukace ni da kawo wadanda za su tsaya min, in mika fasfo di na, kuma suna zargi na ne da laifin halasta kudaden haram, da almubazaranci da kudaden jama'a."

Dokpesi ya kara da cewa shi dan kasa ne na gari, kuma yana da karfin imani.