ECB zai habaka tattalin arzikin kasashen Yuro

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption ECB ya ce zai yunkura domin habaka tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudaden bai daya na Yuro

Babban bankin turai ECB ya sanar da shirinsa na kara himma domin farfado da tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin bai daya na Yuro.

Yanzu haka bankin ya rage kudaden ruwansa, sannan zai fadada shirinsa na siyan kadarori da ake wa lakabi da (quantitative easing).

Babban bankin ya ce hauhawar farashin kayayyakin da ake samu bai kai kaso daya cikin dari ba, a saboda haka ya yi kadan.

Bankin na ECB ya cigaba da cewa yunkurin nasa da zai fara yi zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasashen da ke amfani da kudin na Yuro.

Kazalika babban bankin ya ce yana so ya kara zuba jari da kirkirar ayyukan yi da kuma habaka kayayyakin da ake samarwa.