An kama wasu manyan jami'an FIFA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin jami'an FIFA da karbar hanci.

Gwamnatin Switzerland ta ce an kama manyan jami'an hukumar kwallon kafar duniya, FIFA biyu a ci gaba da binciken da ake yi kan zargin karbar hanci a hukumar.

Ma'aikatar shari'a ta kasar ta ce an kama mutanen biyu ne a Zurich bayan Amurka ta nemi a kama su.

A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce ana zargin mutanen biyu, wadanda ba a fadi sunayensu ba, da "karbar hanci na miliyoyin dala".

Tun da farko dai, 'yan sandan kasar sun kai samame a wani Otal da ke Zurich inda suka kama wasu mutane a watan Mayu lokacin da aka fara yin binciken.