China za ta bai wa Afirka $60bn

Hakkin mallakar hoto Xinhua

Shugaban kasar China Xi Jinping ya ce kasarsa za ta bai wa kasashen Afirka tallafin $60bn domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Mista Xi ya bayar da sanarwar ce a wajen taron da China ke yi da kasashen Afirka a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Ya kara da cewa kudaden sun hada da bashin da babu ruwa a cikinsa da daukar nauyin masu karo karatu daga nahiyar Afirka da kuma bai wa dubban 'yan Afirka horo kan kasuwanci.

Shugaban na China ya ce kasarsa za ta soke bashin da take bin kasashen Afirka da ke cikin talauci.

China ita ce kasar da ta fi yin huldar kasuwanci da Afirka, sai dai jarin da take zuba wa a nahiyar ya fadi da kusan kashe 40 cikin dari a watannin shida na farkon wannan shekarar.