Masu fama da cutar AIDS sun koka

Hakkin mallakar hoto AFP

Mutane masu fama da cutar da ke karya garkuwar jiki ko SIDA a jihar Bauchi da Najeriya, na korafin cewa hukumomi a jihar suna karbar kudin jinya daga wajensu, sabanin yadda tsarin kasa da kasa ya tanadar na yi musu hidimomin jinya a kyauta.

Sun ce lamarin ya sa suna fuskantar matsi wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai hukumomi a jihar na cewa kungiyoyin agaji na kasashen waje ne suka fara janye tallafin da suke bayarwa na yaki da cutar.

Sun ce hakan ne ya sa suke karbar wasu kudaden gwaje-gwaje daga hannun masu dauke da cutar, yayin da gwamnati ke daukar wasu bangarori na dawainiyarsu.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai aka yi bikin ranar yaki da cutar a duniya.