Kotu ta samu Pistorius da laifin kisan kai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Pistorius zai iya fuskantar daurin shekara 15 a gidan yari.

Kotun daukaka kara ta Afirka ta Kudu ta samu dan tseren nan na kasar, Oscar Pistorius da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp.

Kotun ta yi watsi da hukuncin da wata kotun daukaka kara ta kasar ta yanke cewa Pistorius ya aikata kisan ne ba da gangan ba.

Pistorius zai yi fuskantar hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari.

A watan Fabrairun shekarar 2013 Pistorius ya harbi Reeva Steenkamp sau hudu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.

Yanzu dai ana yi masa daurin-talala ne bayan ya kwashe shekara daya a cikin daurin da aka yi masa na shekara biyar.

Pistorius zai koma kotu domin a sake yanke masa wani hukuncin.