An kashe mutane 12 a Masar

Image caption Rahotanni sun ce mutumin da ya jefa bam din ya taba yin aiki a gidan sayar da abincin.

'Yan sandan kasar Masar sun ce akalla mutane 12 ne suka mutu a birnin Alkahira bayan wani dan bindiga ya jefa bam cikin wani gidan sayar da abinci.

Sai dai wasu rahotanni na cewa mutanen da suka mutu sun kai 18.

Kafafen watsa labaran kasar sun ce lamarin ya auku ne a yankin Agouza.

'Yan sandan sun ce gidan ya kama da wuta bayan dan bindigar ya jefa bam din.

Wani rahoto ya ce mutumin da ya jefa bam din ba shi da aikin yi bayan masu gidan sayar da abincin sun kore shi daga aiki.