An amince Jamus ta fara luguden wuta kan IS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamus na dari-darin shiga wannan yaki

'Yan majalisar dokokin Jamus sun amince gwamnatin kasar ta fara kai hare-hare ta sama a kan mayakan kungiyar IS da ke Syria.

Za a tura jiragen yakin kasar samfurin Tornado da kuma jiragen ruwa, sannan a tura sojoji 1,200 zuwa Syria.

Sai dai ba za su shiga cikin fafatawar da ake yi ta kai-tsaye ba.

Hakan wani goyon baya ne da rokon da Faransa ta yi wa kasar na neman hadin kan kasashe, bayan hare-haren da aka kai a Paris a watan jiya.

Jamus na dari-darin tura sojojinta, amma ministocin kasar sun yi imanin cewa mayakan IS na shirin kai wa kasar hari.