Boko Haram: An kashe mutane 4 Borno

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter

A kalla mutane hudu ne suka mutu yayin da kimanin takwas suka jikkata a lokacin da wasu 'yan kunar bakin wake suka tayar da bama-bamai a garin Kimba da ke karamar hukumar Biu da kuma Sabon gari da ke karamar hukumar Dambuwa a jihar Borno, a Najeriya.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibiti na garin Biu inda suke karbar magani.

Al'amarin ya faru ne a ranar Juma'a da maraice.

Shugaban hukumar bayar da agajin gagagwa ta arewa maso gabashin Nigeria Muhammad Kanar ya shaidawa BBC cewa wadanan wurare biyu da aka kai wa hari, wurare ne da suke shirin kafa sansanoni domin a karawa mutane kaimin komawa gidajensu.