Za a zabi sabon shugaban PDP

Image caption Jam'iyyar PDP ta fada cikin rikici tun bayan zaben shugaban kasa.

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta ware ranar 19 ga watan Maris na shekarar 2016 domin zaben shugabanta a taron da manyan jami'anta za su yi a Abuja.

Jam'iyyar ta dauki wannan mataki ne a wani kwarya-kwaryar taro da 'yan kwamitin gudanarwarta suka yi ranar Alhamis da daddare.

A wata sanarwa da kakakinta, Chief Olisa Metuh, ya fitar jam'iyyar ta tabbatar da cewa za a zabi sabon shugaban jam'iyyar a watan Maris.

Ta kara da cewa a ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 2016 za a yi taron fitar da wakilan da za su halarci taron jam'iyyar a matakin mazabu, sannan a gudanar da irinsa a matakin kananan hukumomi da jihohi a ranakun biyar da 12 ga watan Maris.

Mista Metuh ya ce a ranar 16 ga watan Maris din ne za a yi zaben a matakin yankuna, kafin a yi na kasa ranar 19 ga watan na Maris.

Jam'iyyar ta PDP dai ta fada cikin rikici tun bayan zaben shugaban kasa a watan Maris na shekarar 2015, inda wasu 'yan asalin yankin arewa maso gabashin kasar ke yin adawa da nada Uche Secondus -- daga kudancin kasar -- a matsayin shugaban-riko bayan saukar Ahmed Adamu Mu'azu daga jihar Bauchi.