Jimmy Floyd Hasselbaink zai zama kociyan QPR

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption QPR zata nada Jimmy Floyd Hasselbaink a matsayin kociyanta

Queens Park Rangers na shirin nada Jimmy Floyd Hasselbaink a matsayin sabon kociyan su.

Yanzu haka dai Jimmy Floyd Hasselbaink shi ne kociyan Burton Albion.

Gidan rediyon BBC ya rawaito cewa tsohon dan wasan gaba na Chelsea zai samu horo a kulob din west London a ranar Juma'a.

Mai kimanin shekaru 43, Jimmy Floyd Hasselbaink ya jagoranci kulob din Burton a gasar wasan League Two a kakar wasannin ta bara, kuma yanzu haka kulob din nasa shi ne kan gaba a teburin gasar League One.

Neil Warnock shi ne mai rikon kwarya a kulob din na QPR tun bayan da aka kori Chris Ramsey a ranar 4 ga watan Nuwamba, kuma ya jagoranci kulob din a wasan da suka yi nasara a kan Reading a ranar Alhamis.