Sanatoci sun fusata masu amfani da intanet

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption 'Yan majalisar dattawan sun ce ya kamata a daure masu amfani da shafukan intanet idan sun karya doka.

Masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet sun fusata saboda kudurin dokar da 'yan majalisar dattawan Najeriya ke shirin amincewa da shi kan daure masu mu'amala da shafukan idan sun karya doka.

Idan aka zartar da kudurin dokar dai, masu mu'amala da shafukan sada zumuntar da suka yi wa wani "kazafi" za su iya shan daurin shekara biyu a gidan yari.

Dan majalisar ya da gabatar da kurin, Bala Ibn Na'Allah ya ce bai kamata a rika barin 'yan kasar suna cin zarafin mutane musamman a shafukan sada zumunta ba.

A cewarsa, babu wata kasa a duniya da za ta yarda 'ya'yanta su rika rubuce-rubuce da ke "yin zarge-zarge na babu gaira babu dalili" ba tare da an hukunta su ba.

Kudurin dokar ya bukaci "A yi daurin shekara bakwai ko tarar N5m ga duk mutumin da -- da gangan -- ya watsa labaran karya wadanda za su iya yin barazana ga tsaron kasa ko kuma labaran da za su sa 'yan kasa su yi wa gwamnati tawaye".

Haka kuma kudurin ya nemi "A yi daurin shekara biyu ko sanya tarar N2m kan duk wanda ya yi amfani da sakon tes da Twitter, WhatsApp da ma sauran shafukan sada zumunta wajen yin zage-zage da zummar harzuka mutane".

Sai dai masu amfani da shafukan sun kalubalanci 'yan majalisar dattawan, suna masu cewa kudurin dokar "wani yunkuri ne na hana 'yan Najeriya fadin albarkacin bakinsu".

Daya daga cikinsu, Malam Abdul Aziz Ahmad, ya shada wa BBC cewa da ma can akwai dokar da ta hana bata sunan wani, don haka abin da sanatocin ke yi soki-burutsu ne kawai.

Wannan batu dai ya sanya masu amfani da shafin Twitter a Najeriya sun kirkiro da maudu'i mai suna #NoToSocialMediaBill, wato "muna kyamar dokar da za ta yi wa masu amfani da shafukan sada zumunta tarnaki".