Kwanaki 600 da sace matan Chibok ba labari

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Masu fafutukar ganin an ceto matan Chibok

Kungiyar Bring Back Our Girls mai fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok ta ce ta na fatan gwamnatin Najeriya za ta ceto 'yan mata 219 dake hannun kungiyar Boko Haram zuwa karshen watan Disamba.

Kungiyar ta sanar da hakan ne a taron da ta yi a Unity Fountain da ke babban birnin kasar Abuja, don tunawa da cika kwanaki 600 da sace 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta yi.

Wasu daga cikin kawayen 'yan matan sun ce rashin ceto 'yan matan har zuwa wannan lokaci, yana kara sa su zama cikin fargaba.

Jagororin kungiyar sun ce watanni shida da kama aikin shugaba Buhari, hankalinsu ba zai kwantaba sai in an dawo musu da 'yan matan.