Kwamishina zai yi shekara 10 a gidan yari

Image caption An yankewa tsohon kwamishina zaman gidan kaso na shekaru 10

Wani tsohon kwamishinan kananan hukumomi a jihar Adamawa zai zauna gidan yari na tsawon shekaru goma.

Babbar kotun tarayya ta jihar ce ta yanke wa Mr John Elias Babani hukuncin saboda samunsa da laifin sama da fadi da kudaden gwamnatin jihar da ya kai Naira miliyan hamsin da daya da dubu dari biyar a lokacin da ya ke rike da mukamin kwamishinan kananan hukumomi na jihar ta Adamawa

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2013.

An kuma gurfanar da shi ne tare da wasu mutane biyu wadanda kotun ta wanke su.

Mai shari'a Bilkisu Bello Aliyu ta yankewa mai laifin hukuncin zaman gidan yarin ne bisa laifuka biyu da kotun ta same shi da aikatawa.

Kazalika kotun ta umarci mai laifin ya dawo da kudin da ya yi sama da fadin da su ga asusun hadaka na kananan hukumomin da gwamnatin jihar Adamawa.