Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

China: Kashedin gurbatar yanayi a Beijing

Hukumomi a Beijing, babban birnin China sun yi gargadi dangane da gabatowar mummunan hazo dake da alaka da gurbatar yanayi, wanda yake lullube birnin.

An umarci makarantun Piramare da kuma da kuma na sakandire kada su fitar da yara waje domin yin wasanni daga farkon wannan makon.

Cikin makon jiya ne dai aka bada gargadi mafi tsauri akan gurbatar iska a birnin karon farko a wannan shekarar.

A 'yan kwanakin nan dai yanayin hazon ya dan tsagaita, amma kuma ya sako dawowa a arewa da kuma tsakiyar China.

Hazon dake hade da hayaki dake turnikewa ya zama babbar matsala a mafi yawan biranen China.

Kuma lamarin yana yin illa ga lafiyar jama'a, musamman ma yara kanana.

Domin jin karin bayani, Isa Sanusi yayi hira da Tukur Hassan Tinglin dalibi a birnin Beijing.