Facebook zai bullo da tsarin yada bidiyo kai tsaye

Image caption Tsarin yada bidiyo kai tsaye a Facebook

Facebook ya fara bullo da wani tsari a shafin da zai rika bai wa masu amfani da shi damar yada hotunan bidiyo kai tsaye ga masu bin su a shafukansu.

Wasu taurarin mawaka da manyan mutane sun fara amfani da tsarin watanni da suka gabata.

Aikawa da sakon bidiyo kai tsaye ta wayoyin tafi da gidanka shi ne tsarin fasaha da yafi karbuwa a wannan shekarar, inda a ka fi amfani da manhajar Periscope da Meerkat mallakin Twitter.

A 2014, katafaren shagon sayar da kayayyaki ta intanet, Amazon ya biya dala biliyan daya don bayar da damar buga wasannin kwamfuta ta intanet kai tsaye.

Yanzu 'yan tsirarun mutane a Amurka ne za su yi amfani da tsarin yada bidiyon kai tsaye na Facebook din, kuma a wayoyin iPhone kadai.

Kamfanin na Facebook ya ce zuwa wani lokaci nan gaba, zai fadada amfani da tsarin ta yadda duk masu amfani da shafin Facebook za su samu damar yin hakan.