"Saudi na taimakawa masu muguwar akida"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel

Mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Sigmar Gabriel ya bukaci kasar Saudiyya da ta daina daure wa kungiyoyin masu tayar da kayar baya 'yan kishin Islama gindi.

Mista Gabriel ya ce Saudiyya tana taimakawa kungiyoyin ne ta hanyar ba masallatan kungiyoyin kudade a wasu kasashe.

Ya shaida wa wata jaridar kasar Jamus cewa 'yan kishin Islama masu hadarin gaske suna shiga Jamus daga Masallatan da Saudiyya ke daukar dawainiyarsu masu yada akidar Wahabiyanci.

Ofishin jakadancin Saudiyya a Berlin ya ce kasarsa tana da burin magance yada tsatssaurar akida a tsakanin matasa.

A cikin makon jiya gwamnatin Jamus din ta ja kunnen hukumar leken asirinta a kasashen waje saboda kakkausar sukar da ta yi wa Saudiyya.